WANENE YA HALICCE NI? KUMA SABODA ME?Ko wanne abu yana nuni akan akwai mahalicci
wagga madda an tarjamata zuwa
- English - English
- български - Bulgarian
- português - Portuguese
- svenska - Swedish
- العربية - Arabic
- Wikang Tagalog - Tagalog
- Kurdî - Kurdish
- Français - French
- हिन्दी - Hindi
- español - Spanish
- čeština - Czech
- Русский - Russian
- Bahasa Indonesia - Indonesian
- ગુજરાતી - Unnamed
- অসমীয়া - Assamese
- አማርኛ - Amharic
- ไทย - Thai
- Deutsch - German
- Tiếng Việt - Vietnamese
- italiano - Italian
- فارسی دری - Unnamed
- বাংলা - Bengali
- Shqip - Albanian
- 中文 - Chinese
- Nederlands - Dutch
- Kiswahili - Swahili
- اردو - Urdu
- پښتو - Pashto
- සිංහල - Sinhala
- magyar - Hungarian
- ქართული - Georgian
- bamanankan - Bambara
- Akan - Akan
- Lingala - Unnamed
- ئۇيغۇرچە - Uyghur
- bosanski - Bosnian
nau o, i
Full Description
WANENE YA HALICCE NI? KUMA SABODA ME?Ko wanne abu yana nuni akan akwai mahalicci
Wa ya halicci sammai da kasa da abinda ke tsakanin su na halittu masu girma wadanda ba'a iya gane yawansu?
Wa ya kera wannan nagartaccan tsarin kayatacce a sama da kasa ?
Wa ya halicci mutum ya kuma ba shi ji da gani da hankali? Ya sanya shi mai iko akan tsururutar ilimai da gane hakikanin abubuwa ?
Yaya zaka fassara wannan kira gwananna dake na'urorin (gabban) jikinka da suke kuma a jukkunan kasantattu suna aiki? kuma wanene ya kage su?
Ta yaya wannan kasantacce mai girma yake tsaruwa kuma yake tabbatuwa tare da ƙa'idojin sa, waɗanda suke kiyaye shi, kiyaye wa ta ƙwarewa tsawon shudewar waɗannan shekaru?
Wa ya sanya wadannan tsare-tsare wadanda suke tafiyar da wannan halittar (rayuwa da mutuwa, bibikon rayuwa, dare da yini, canjin lokuta …
Shin wannan kasantacce (halittu) shi ne ya halicci kansa? Ko ya zo ne ba daga wurin kowa ba? Ko kuma an same shi kawai kwatsam?
Saboda me mutum yake yin imani da abubuwan da ba ya ganisu, kamar: (Tunani hankali, rai, ji a jika, da so.) a she ba saboda yana ganin alomominsu ba ne? To tayaya mutum zai yi musun samuwar Mahaliccin wadannan abubuwa masu girma, alhalin yana ganin alamomi na halittarsa da aikinsa da kuma rahamarsa?
Babu wani mutum da zai yarda a ce da shi: Ai wannan gidan kawai ya samu ne ba tare da wani ne ya gina shi ba! Ko a ce da shi: Ai babu ita ce ta samar da wannan gidan! To ta yaya wasu daga cikin mutane za su gasgata wanda yake cewa wannan duniyar mai girma ta zo ne ba tare da Mahalicci ba?. Tayaya mai hankali zai yarda a ce da shi wannan ginin (na sama da ƙasa) wanda ke cike da ƙwarewa ya samu ne haka kawai?
Allah - Madaukakin sarki - Ya ce:(أَمۡ خُلِقُواْ مِنۡ غَيۡرِ شَيۡءٍ أَمۡ هُمُ ٱلۡخَٰلِقُونَ، أَمۡ خَلَقُواْ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَۚ بَل لَّا يُوقِنُونَ). ko an halicce su ba tare da mai halitta ba, ko kuma su ne masu halitta ko sun halicci sammai da kassai, ba hakaba, su ba sa tabbatarwa{32 : 52}
Allah Mai tsarki kuma Madaukaki
Akwai Ubangiji kuma mahalicci guda daya, yanada sunaye da suffofi masu yawa masu girma, wadanda suke nuna cikarsa, yana daga sunsyensa: mahalicci, mai jinkai, mai azurtawa, mai karamci, da kuma sunsnsa "ALLAH' wanda shi ne suna mafi shahara daga sunayensa Ubangiji tsarkakakke madaukaki, ma'anarsa: wanda ya cancanci bauta shi kadai, ba shi da abokin tarayya.
Allah - Maɗaukakin sarki - a ckin Alkur'ani mai girma Ya ce:﴿قُلۡ هُوَ ٱللَّهُ أَحَدٌ "Ka ce: "Shi ne Allah Makaɗaĩci."* ٱللَّهُ ٱلصَّمَدُ *Allah wanda ake nufin Sa da buƙata*لَمۡ یَلِدۡ وَلَمۡ یُولَدۡ *Bai haifa ba kuma ba'a haife Shi ba*وَلَمۡ یَكُن لَّهُۥ كُفُوًا أَحَدُۢ﴾ *Kuma babu wani da yake kini a gareShi{1-4 :112}.
kuma Allah Madaukaki ya ce:﴿اللَّهُ لا إِلَهَ إِلَّا هُوَ الْحَيُّ الْقَيُّومُ لا تَأْخُذُهُ سِنَةٌ وَلا نَوْمٌ لَهُ مَا فِي السَّمَوَاتِ وَمَا فِي الأَرْضِ مَنْ ذَا الَّذِي يَشْفَعُ عِنْدَهُ إِلَّا بِإِذْنِهِ يَعْلَمُ مَا بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَمَا خَلْفَهُمْ وَلا يُحِيطُونَ بِشَيْءٍ مِنْ عِلْمِهِ إِلَّا بِمَا شَاءَ وَسِعَ كُرْسِيُّهُ السَّمَوَاتِ وَالأَرْضَ وَلا يَئُودُهُ حِفْظُهُمَا وَهُوَ الْعَلِيُّ الْعَظِيمُ﴾ {Allah, bãbu wani Ubangiji fãce Shi, Rãyayye, Mai tsayuwa da kõme, gyangyaɗi bã ya kãma Shi, kuma barci bã ya kãma Shi, Shi ne da abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa. Wanene wanda yake yin cẽto a wurinSa, fãce da izninSa? Yana sanin abin da yake a gaba gare su da abin da yake a bãyansu. Kuma bã su kẽwayẽwa da kõme daga ilminSa, fãce da abin da Ya so. KursiyyunSa ya yalwaci sammai da ƙasa. Kuma tsare su bã ya nauyayarSa. Kuma Shi ne Maɗaukaki, Mai girma}{255:2}.
Suffofin Ubangiji tsarkakakke madaukaki
Ubangiji shi ne wanda ya halacci kasa ya kuma horeta, ya sanya ta ingantacciya ga halittarsa ( wacce za su iya rayuwa a kanta) shi ne kuma wanda ya halicci sammai da abinda ke tsakaninsu na halittu masu girma, kuma ya sanya rana da wata da dare da wuni, wannan gwanannan tsari wanda yake nuni a bisa girmansa.
Ubangiji shi ne wanda ya hore mana iska, wacce ba za mu iya rayuwa ba sai da ita, shi ne kuma wanda yake saukar da ruwan sama a gare mu, ya hore mana koguna da koramu, shi ne wanda yake ciyar damu abinci a yayin da muke yantayi a cikkunan iyayenmu, ba wani karfi a gare mu, shi ne kuma yake sanya jini da yake gudana a jijiyoyin mu, ya sanya zuciyoyin mu suna bugawa koda yaushe, tun daga ranar haihuwarmu zuwa mutuwar mu.
Allah - Madaukakin sarki - Ya ce:﴿وَاللَّهُ أَخْرَجَكُمْ مِنْ بُطُونِ أُمَّهَاتِكُمْ لَا تَعْلَمُونَ شَيْئًا وَجَعَلَ لَكُمُ السَّمْعَ وَالْأَبْصَارَ وَالْأَفْئِدَةَ لَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ﴾ Kuma Allah ne Ya fitar da ku daga cikunan iyãyenku, ba da kunã sanin kõme ba, kuma Ya sanya muku ji da gannai da zukãta, tsammãninku zã ku gõde.(78 :16)
Ubangiji abin bautawa, babu makawa lalle ya siffantu da siffofin cika
Mahaliccin mu ya azurta mu da hankula, da za su gane girman sa, ya kuma dasa mana halittar asali da take nuni a bisa cikarsa, kuma cewa shi ba zai yi wu ba ya siffantu da tawaya.
Lalle tilas ibada ta kasance ga Allah madaukaki shi kadai, shi ne cikakke wanda ya cancanci a bauta masa, duk abinda aka bautawa da ba shi ba, to shi batacce ne kuma tauyayye, mutuwa da karewa za su bijiro masa.
Ba zai yi wu ba abin bautawa ya kasnce mutum ko gunki ko bishiya ko dabba.
Ba ya dacewa ga mai hankali, ya bautawa wani sai cikakke, to, ta yaya zai bautawa abin halitta wanda yake kasa da shi!
Ba zai yi wu ba Ubangiji ya kasance dantayi a ckin wata mace, kuma a haife shi kamar yadda ake haihuwar jarirai!
Ubangiji shi ne wanda ya halicci halittu, halittu suna cikin damkarsa, kuma suna karkashin rinjayin sa, ba zai yi wu dan Adam ya cutar da shi ko wani ya azabtar da shi ko ya kaskantar da shi ba !
Ba zai yi wu ba Ubangiji ya mutu!
Ubabgiji shi ne wanda ba ya mantuwa, ba ya bacci, ba ya cin abinci, shi mai girma ne, ba zai yi wu ba mata ta kasance a gare shi ba, ko da mahalicci yana da siffofin girma, ba zai yi wu ba har abada ya siffantu da bukata ko tawaya, dukkan nassoshi wadanda a ckinsu akwai abinda yake sabawa girman mahalicci daga abinda ake dangantawa zuwa annabawa, su nassoshi ne wadanda aka jirkita (ma'anarsu) ba su zamo daga ingantaccen wahayi ba,wanda annabi Musa da Isa da wasu annabawan suka zo da shi ba, tsira da aminci ya tabbata a gare su
Allah - Madaukakin sarki - Ya ce:يَا أَيُّهَا النَّاسُ ضُرِبَ مَثَلٌ فَاسْتَمِعُوا لَهُ إِنَّ الَّذِينَ تَدْعُونَ مِنْ دُونِ اللَّهِ لَنْ يَخْلُقُوا ذُبَابًا وَلَوِ اجْتَمَعُوا لَهُ وَإِنْ يَسْلُبْهُمُ الذُّبَابُ شَيْئًا لَا يَسْتَنْقِذُوهُ مِنْهُ ضَعُفَ الطَّالِبُ وَالْمَطْلُوبُ (73) Ya ku mutãne! An buga wani misãli, sai ku saurãra zuwa gare shi. Lalle ne waɗanda kuke kira baicin Allah, bã zã su halitta ƙudã ba, kõ da sun tãru gare shi, kuma idan ƙudãn ya ƙwãce musu wani abu, bã zã su kuɓutar da shi ba daga gare shi. Mai nẽma da wanda ake nẽman gare shi sun raunana.مَا قَدَرُوا اللَّهَ حَقَّ قَدْرِهِ إِنَّ اللَّهَ لَقَوِيٌّ عَزِيزٌ (74) Ba su girmama Allah hakikanin girmanSa ba. Lalle ne Allah, haƙĩƙa, Mai ƙarfi ne, Mabuwãyi.{74,73 :22}
Shin zai yi wu a hankalce mahalicci ya bar mu, ba tare da wahayi ba?
Shin zai yi wu a hankalce, ace Allah ya halicci duk wadannan halittu ba tare da wata manufa ba, shin ya halicce su don wasa, ga shi kuma shi ne gwani masani?
Shin zai yi wu a hankalce cewa, wanda ya halicce mu da wannan kyautataccen tsari, ya kuma hore mana abinda ke cikin sammai da kasa, a ce ya halicce mu, ba tare da wata manufa ba, ko ya bar mu ba tare da amsa mafi muhimmancin tambayoyi ba, wadanda za su ja hankalin mu, misalin: saboda me muke a nan? menene zai kasance bayan mutuwa? menene manufar halittar mu?
Ba haka ba, Allah ya aiko mazanni, don mu san manufar samuwar mu, kuma me yake so a gare mu?
Allah ya aiko manzanni don su bamu labarin cewa shi kadai yake, wanda ya cancanci a bauta masa, kuma mu san yaya za mu bauta masa, kuma su isar mana da umarninsa da haninsa, su koya mana kyawawan dabi'u wadanda idan muka yi riko da su rayuwar mu za ta daukaka, alkhairai da albarkatu za su game ta.
Hakika Allah ya aiko manzanni masu yawa misalin (annabi Nuhu, annabi Ibrahim, annabi Musa, annabi Isa) kuma Allah ya baiwa wadannan manzanni ayoyi da mu'ujizozi wadanda suke nuni a bisa gaskiyar su, kuma suke tabbatar da cewa su manzanni ne daga gurin mahalicci.
Karshen manzanni shi ne annabi Muhammad- tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- hakika Allah ya saukar da Alkur'ani a gare shi.
Kuma hakika Manzanni sun ba mu labari a bayyane cewa wannan rayuwa jarrabawa ce, kuma lalle rayuwa ta hakika zata kasance ne bayan mutuwa
Kuma cewa a lahira akwai Aljanna ga muminai wadanda suka bautawa Allah shi kadai ba tare da abokin tarayya a gare shi ba, kuma suka yi imani da dukkanin manzanni, haka nan kuma a lahira akwai wuta wacce Allah ya tanadeta ga kafirai, wadanda suka bautawa wasu alloli tare da Allah ko suka kafirce wa mu'ujizozin manzanni daga manzannin Allah.
Allah - Madaukakin sarki - Ya ce:
يَابَنِي آدَمَ إِمَّا يَأْتِيَنَّكُمْ رُسُلٌ مِنْكُمْ يَقُصُّونَ عَلَيْكُمْ آيَاتِي فَمَنِ اتَّقَى وَأَصْلَحَ فَلَا خَوْفٌ عَلَيْهِمْ وَلَا هُمْ يَحْزَنُونَ (35) Yã ɗiyan Ãdam! Ko dai wasu manzanni, daga cikinku, su jẽ muku, sunã gaya muku ayõyiNa to, wanda ya yi taƙawa, kuma ya gyara aikinsa, to, bãbu tsoro a kansu, kuma bã su yin baƙin ciki.وَالَّذِينَ كَذَّبُوا بِآيَاتِنَا وَاسْتَكْبَرُوا عَنْهَا أُولَئِكَ أَصْحَابُ النَّارِ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ (36) Kuma waɗanda suka ƙaryatã game da ãyõyinMu, kuma suka yi girman kai daga gare su, waɗannan sũ ne abõkan wuta, sũ, a cikinta madawwama ne.{35,36 :7}
Kuma tsarki ya tabbatar masa ya ce:﴿ أَفَحَسِبْتُمْ أَنَّمَا خَلَقْنَاكُمْ عَبَثًا وَأَنَّكُمْ إِلَيْنَا لَا تُرْجَعُونَ ﴾ {Shin, to, kun yi zaton cẽwa Mun halicce ku ne don wãsa kuma lalle ku, zuwa gare Mu, bã zã ku kõmo ba} ?{115:23}
ALKUR'ANI MAI GIRMA
Alkur'ani mai girma shi zancan Allah ne madaukaki, wanda ya saukar da shi ga karshen manzanni annabi Muhammad, kuma shi ne mafi girman mu'ujiza da take nuni a bisa gaskiyar annabtar annabi Muhammad-tsira da aminci su tabbata a gare shi - gaskiya ne a hukunce-hukuncen sa, gaskiya a labarunsa, kuma hakika Allah ya kalubalanci masu karyatawa da su zo da koda da sura daya irin wannan Alku'ani, sai suka gajiya a bisa haka, saboda kyan salon sa da kyautatuwar lafuzan sa, kuma hakika ya kunshi manya-manyan dalilai na hankali da hakikanin na ilimi, wadanda suke nuni a bisa cewa wannan Littafi (Alkur'an) ba zai yi wu a ce ya kasan ce daga samarwar dan adam ba, a'a shi zancen Ubangijin dan adam ne, tasrki da daukaka sun tabbatar masa
ME YASA MANZANNI SUKE DA YAWA?
Hakika Allah ya aiko manzanni tun farkon zamani, don su kira mutane zuwa ga Ubangijin su, kuma su isar musu da umarninsa, da hane-hanan sa, kiran su (manzanni) gaba daya ya kasance ne (akan) bautar Allah ne shi kadai, mai girma da daukaka, duk sa'adda wata al'umma ta fara barin ko canza abinda manzonta ya zo da shi, na umarnin kadaita Allah, sai Allah ya dorawa wani manzon daban, don ya gyara matafiyar, ya kuma maida mutane zuwa halitta ta asali kubutacciyya, ta hanyar kadaita Allah, da yi masa biyayya, har Allah ya cika manzanni da annabi Muhammad tsira da aminci su tabbata a gare shi, wanda ya zo da shari'ah madawwamiya, mai gamewa ga dukkanin 'yan adam har zuwa ranar alkiyama,(shari'ah) ce cikakkiya ta kuma shafe shari'o'in da suke gabaninta, Ubangiji- ya girmama kuma ya daukaka- ya lamincewa wannan shari'ar da sakon wanzuwa da dawwama har zuwa ranar alkiyama.
Saboda haka mu musulmi muna imani- kamar yadda Allah ya umarta- da dukkanin manzanni da Littattafan da suka gabata.
Allah - Madaukakin sarki - Ya ce:﴿ءَامَنَ ٱلرَّسُولُ بِمَاۤ أُنزِلَ إِلَیۡهِ مِن رَّبِّهِۦ وَٱلۡمُؤۡمِنُونَۚ كُلٌّ ءَامَنَ بِٱللَّهِ وَمَلَـٰۤىِٕكَتِهِۦ وَكُتُبِهِۦ وَرُسُلِهِۦ لَا نُفَرِّقُ بَیۡنَ أَحَدࣲ مِّن رُّسُلِهِۦۚ وَقَالُوا۟ سَمِعۡنَا وَأَطَعۡنَاۖ غُفۡرَانَكَ رَبَّنَا وَإِلَیۡكَ ٱلۡمَصِیرُ﴾ Manzo ya yi imani da abinda aka saukar izuwa gare shi daga Ubangijin sa da muminai, kowanne ya yi imani da Allah da mala'ikun sa da littatafan sa da manzannin sa, ba ma rabewa tsakanin wani daga manzannin sa, suka ce mun ji kuma mun yi biyayya, muna neman gafarar ka Ubangijin mu makoma tana gare ka.[2: 285]. {285 :2}.
Mutum ba zai kasance mumini ba, har sai ya yi imani da dukkanin manzanni
Allah shi ne wanda ya aiko manzanni, wanda ya kafirce da wani sako guda daya daga gare su, to, hakika ya kafirta da dukkannin su, babu wani zunubi mafi girma fiye da mutum ya ki karbar wahayin da Allah ya yi, babu makawa yin imani da dukkanin manzanni domin shiga aljanna.
Wajibi akan kowa a wannan zamani ya yi imani da dukkan manzannin Allah, hakan kuma ba zai kasance ba sai ya yi imani, kuma ya bi (annabi) na karshen su kuma cikamakin su, annabi Muhammad tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi.
Allah ya ambata a cikin Alkur'ani mai girma cewa duk wanda ya ki yin imani da wani manzo daga cikin manzannin Allah, shi mai kafircewa Allah ne, mai karyatawa ne ga wahayinsa.
Ka karanta aya mai zuwa:"إنَّ الَّذِينَ يَكْفُرُونَ بِاللَّهِ ورُسُلِهِ ويُرِيدُونَ أنْ يُفَرِّقُوا بَيْنَ اللَّهِ ورُسُلِهِ ويَقُولُونَ نُؤْمِنُ بِبَعْضٍ ونَكْفُرُ بِبَعْضٍ ويُرِيدُونَ أنْ يَتَّخِذُوا بَيْنَ ذَلِكَ سَبِيلًا Lalle ne, waɗanda suke kãfircewa da Allah da ManzonSa kuma sunã nufin su rarrabe a tsakãnin Allah da manzanninSa, kuma sunã cẽwa: "Munã ĩmãni da sãshe, kuma munã kãfirta da sãshe." Kuma sunã nufin su riƙi hanya a tsakãnin wannan.أُولَئِكَ هُمُ الكافِرُونَ حَقًّا وأعْتَدْنا لِلْكَفَرَيْنِ عَذابًا مُهِينًا﴾". Waɗannan sũ ne kãfirai sõsai, kuma Mun yi tanadi, dõmin kãfirai, azãba mai walãkantarwa.{150,151 :4}
MENENE MUUSULINCI?
Musulinci shi ne mika wuya ga Allah madaukaki da kadaita shi, da mika wuya a gare shi ta hanyar yi masa biyayyya, da riko ga shari'arsa da yarda da karba.
Hakika Allah ya aiko manzanni don sako guda daya, shi ne: kira zuwa bautar Allah shi kadai babu abokin tarayya a gare shi.
Musulunci shi ne addinin dukkanin annabawa, kiransu guda daya ne, shari'o'in su ne mabanbanta, musulmai a yau su kadai ne masu riko da ingaantaccen addini, wanda dukkanin annabawa suka zo da shi, sakon musulinci a wannan zamani shi ne gaskiya, Ubangiji da ya aiko annabi Ibrahim da annabi Musa da annabi Isa, shi ne wanda ya aiko cikamakin manzanni annabi Muhammad, kuma hakika shari'ar Musulunci ta zo mai shafewa ga abinda ya rigayeta na shari'o'i.
Lalle dukkanin addinai wadanda a yau mutane suke bauta da su banda Musulunci, addinai ne da 'yan adam suka samar da su, ko kuma sun kasance addinan Allah ne, sannan sai hannanyen 'yan adam su ka yi wasa da su, sai suka wayi gari ababan cudanyawa da dandazon tasuniyoyi da suka dinga gadarwa junan su, da kuma kokarin (binciken) 'yan adam, amma akidar musulmai ita akida ce guda daya bayyananniya, ba ta canzawa, yi duba zuwa Alkur'ani mai girma, shi littafi ne guda daya a dukkanin garurruwan musulmi.
Allah - Maɗaukakin sarki - a ckin Alkur'ani mai girma Ya ce:
قُلْ آمَنَّا بِاللَّهِ وَمَا أُنْزِلَ عَلَيْنَا وَمَا أُنْزِلَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَإِسْمَاعِيلَ وَإِسْحَاقَ وَيَعْقُوبَ وَالْأَسْبَاطِ وَمَا أُوتِيَ مُوسَى وَعِيسَى وَالنَّبِيُّونَ مِنْ رَبِّهِمْ لَا نُفَرِّقُ بَيْنَ أَحَدٍ مِنْهُمْ وَنَحْنُ لَهُ مُسْلِمُونَ (84) Ka ce: "Mun yi ĩmãni da Allah kuma da abin da aka saukar mana da abin da aka saukar wa Ibrãhĩma da Isma'ĩla da Is'hãƙa da Yãƙũba da jĩkõki, da abin da aka bai wa Mũsã da ĩsã da annabãwa daga Ubangijinsu, bã mu bambantãwa a tsakãnin kõwa daga gare su. Kuma mũ, zuwa gare Shi mãsu sallamãwa ne."وَمَنْ يَبْتَغِ غَيْرَ الْإِسْلَامِ دِينًا فَلَنْ يُقْبَلَ مِنْهُ وَهُوَ فِي الْآخِرَةِ مِنَ الْخَاسِرِينَ 85). Kuma wanda ya nẽmi wanin Musulunci ya zama addini, to, bã zã a karɓa daga gare shi ba. Kuma shi a Lãhira yana daga cikin mãsu hasãra.[84,85, :3}
ME MUSULMAI SUKE KUDIRCEWA DANGANE DA ANNABI ISA AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARE SHI ?
Shin kasan cewa yana wajaba akan musulmai su yi imani da annabin Allah Isa, su so shi, su girmama shi, su yi imani da sakon sa, wanda shi ne kira zuwa bautawa Allah shi kadai ba shi da abokin tarayya! musulmai suna kudircewa annabi Isa da annabi Muhammaad (tsira da amincin Allah su tabbata agare su) sun kasan ce annabawa ne, kuma an aiko su don su shiryar da mutane zuwa hanyar Allah da hanyar aljanna.
Muna kudircewa annabi Isa - amincin Allah ya tabbata agarea shi ya kasance daga mafi girman manzanni, wadanda Allah madaukakin sarki ya aiko su, kuma muna kudircewa, shi (annabi Isa) an haife shi ne ta yanayi mai gajiyarwa, hakika Allah ya bamu labari a cikin Alkur'ani cewa shi ya halicci annabi Isa ba tare da uba ya kasance a gare shi ba, kamar yadda ya halicci annabi Adam ba tare da uwa ko uba ba, Allah mai iko ne a bisa komai.
Kuma muna kudircewa cewa, annabi Isa ba Allah ba ne, kuma ba dan Allah ba ne, kuma ba'a gicciye shi ba, a'a shi yana raye, Allah ya daga shi zuwa gare shi, don ya sauko a karshen zamani, yana mai hukunci mai adalci, zai kasance tare da musulmai, domin musulmai sun yi imani da kadaitakar Allah, wanda annabi Isa ya zo da ita da dukkanin annabawa.
Hakika Alkur'ani mai girma ya bamu labari cewa, Nasara sun canja sakon annabi Isa, kuma akwai masu canzawar batattu, wadanda suka karkatar kuma suka canja abinda ke cikin Injila, suka kara wasu nassoshi da annabi Isa bai fade su ba, abinda zai gasgata haka kuwa shi ne, yawaitar littafan injila (maban-banta) da kuma samuwar yawaitar warwara (karo da juna) a cikinsu.
Hakika Allah ya ba mu labari cewa annabi Isa ya kasance yana bauta wa Ubangijinsa, bai nemi wani ya bauta masa ba, a'a ya kasance yana umartar mutanesa da su bautawa mahalccinsa, sai dai shaidan ya sanya Nasara suke bautawa annabi Isa, kuma Allah ya ba mu labari a cikin Alkur'ani cewa, shi ba ya gafartawa wani da ya bautawa wanin Allah, kuma lalle annabi Isa ranar alkiyama zai barranta (nisantar da kansa) daga wadanda suka bauta masa, zai ce da su, na umarce ku da ku bautawa mahalcci, ban neme ku da ku bauta min ba. Daga dalilan haka fadarsa madaukakin sarki:
﴿یَـٰۤأَهۡلَ ٱلۡكِتَـٰبِ لَا تَغۡلُوا۟ فِی دِینِكُمۡ وَلَا تَقُولُوا۟ عَلَى ٱللَّهِ إِلَّا ٱلۡحَقَّۚ إِنَّمَا ٱلۡمَسِیحُ عِیسَى ٱبۡنُ مَرۡیَمَ رَسُولُ ٱللَّهِ وَكَلِمَتُهُۥۤ أَلۡقَىٰهَاۤ إِلَىٰ مَرۡیَمَ وَرُوحࣱ مِّنۡهُۖ فَـَٔامِنُوا۟ بِٱللَّهِ وَرُسُلِهِۦۖ وَلَا تَقُولُوا۟ ثَلَـٰثَةٌۚ ٱنتَهُوا۟ خَیۡرࣰا لَّكُمۡۚ إِنَّمَا ٱللَّهُ إِلَـٰهࣱ وَ ٰحِدࣱۖ سُبۡحَـٰنَهُۥۤ أَن یَكُونَ لَهُۥ وَلَدࣱۘ لَّهُۥ مَا فِی ٱلسَّمَـٰوَ ٰتِ وَمَا فِی ٱلۡأَرۡضِۗ وَكَفَىٰ بِٱللَّهِ وَكِیلࣰا﴾ Ya ma'abota littafi kada ku zurfafa a addininku kada ku fadi (wata magana) ga Allah sai gaskiya, kadai masihu Isa dan Maryama manzon Allah ne kuma kalmarsa ce ya jefa ta zuwa Maryama da rai daga gare shi, ku yi imani da Allah, da manznninsa kada ku ce uku ne, ku hanu shi yafi alkhairi a gare ku, kadai Allah Ubangiji ne daya, tsarki ya tabbata a gare shi, Da ya kasance a gare shi, abinda yake cikin sammai da kasa na sa ne, Allah ya isa abin dogoro.{171 : 4}.
Allah Madaukaki ya ce(وَإِذْ قَالَ اللَّهُ يَا عِيسَى ابْنَ مَرْيَمَ أَأَنتَ قُلْتَ لِلنَّاسِ اتَّخِذُونِي وَأُمِّيَ إِلَٰهَيْنِ مِن دُونِ اللَّهِ ۖ قَالَ سُبْحَانَكَ مَا يَكُونُ لِي أَنْ أَقُولَ مَا لَيْسَ لِي بِحَقٍّ ۚ إِن كُنتُ قُلْتُهُ فَقَدْ عَلِمْتَهُ ۚ تَعْلَمُ مَا فِي نَفْسِي وَلَا أَعْلَمُ مَا فِي نَفْسِكَ ۚ إِنَّكَ أَنتَ عَلَّامُ الْغُيُوبِ Kuma a lõkacin da Allah Ya ce: "Yã Ĩsã ɗan Maryama! Shin, kai ne ka ce wa mutãne, 'Ku riƙe ni, ni da uwata, abubuwan bautãwa biyu, baicin Allah?" (Ĩsã) Ya ce: "Tsarkinka yã tabbata! Bã ya kasancewa a gare ni, in faɗi abin da bãbu wani hakki a gare ni. Idan nã kasance nã faɗe shi, to lalle Ka san shi, Kanã sanin abin da ke a cikin raina, kuma bã ni sanin abin da ke a cikin nufinKa. Lalle ne Kai Masanin abubuwan fake ne."{116: 5}
Wanda yake son tsira a lahira, wajibi ne akan sa ya shiga musulunci kuma ya bi annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
Yana daga tabbatattun bayanai wadanda annabawa da manzanni -amincin Allah ya tabbata a gare su - suka hadu a kansu, cewa babu wanda zai tsira a lahira sai musulmai, wadanda suka yi imani da Allah madaukakin sarki, ba su kuma hada bautarsa da wani abu ba, suka yi imani da dukkanin annabawa da manzanni, wadanda suka kasance a zamanin annabi Musa kuma suka yi imani da shi, suka bi koyarwarsa, to su wadannan musulmai ne kuma muminai managarta, sai dai da Allah ya aiko annabi Isa, ya wajaba a kan mabiya (annabi) Musa, su yi imani da annabi Isa, su kuma bi shi, wanda ya yi imani da annabi Isa wadannan musulmai ne managarta, wanda ya ki imani da (annabi) Isa kuma ya ce zan wanzu akan addinin annabi Musa, to wannan ba mumini ba ne, domin ya ki imani da annabin da Allah ya aiko shi, sannan bayan da Allah ya aiko karshen manzanni annabi Muhammad ya wajaba akan kowa ya yi imani da shi, Ubangiji shi ne wanda ya aiko annabi Musa da annabi Isa, shi ne kuma ya aiko cikamakin manzanni annabi Muhammad, duk wanda ya kafirce da sakon annabi Muhammad-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- kuma ya ce zan wanzu a cikin mabiyan annabi Musa ko annabi Isa, to wannan ba mumini ba ne.
Ba ya isuwa mutum ya ce shi yana girmama musulmai, haka nan yin sadaka da taimakon miskinai ba za su ishe shi tsira a lahira ba, a'a ba makawa tilas sai ya kasance mai imani da Allah da littatafan sa da manzanninsa da ranar karshe, har Allah ya karbi hakan daga gare shi! babu wani zunubi mafi girma fiye da hada Allah da wani da kafircewa Allah, da kin imani da wahayi wanda Allah ya saukar da shi, ko kin annabtar karshen annabawansa, annabi Muhammad-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- Yahudawa da Nasara wadanda suka ji aiko (annabi) Muhammad manzan Allah-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- suka ki imani da shi kuma suka ki shiga addinin musulinci, za su kasance a cikin wutar jahannama madawwama a cikinta har abada kamar yadda Allah madaukakin sarki ya ce:
{إِنَّ الَّذِينَ كَفَرُوا مِنْ أَهْلِ الْكِتَابِ وَالْمُشْرِكِينَ فِي نَارِ جَهَنَّمَ خَالِدِينَ فِيهَا ۚ أُولَـٰئِكَ هُمْ شَرُّ الْبَرِيَّةِ} Lalle ne waɗanda suka kafirta daga Ma'abota Littafi da mushirikai suna cikin wutar Jahannama suna madawwama a cikinta. Waɗannan su ne mafi ashararancin halitta.{6 :98}
Alokacin da wani sako ya sauka daga Allah zuwa 'yan adam, ya wajaba akan kowanne daya da ya ji (bayanin) Musulunci ya kuma ji (bayanin) annabin karshe annabi Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-, ya yi imani da shi, kuma ya bi shari'ar sa, ya yi masa biyayya a umarninsa da haninsa, saboda haka wanda ya ji wannan sako na karshe kuma ya ki shi, to Allah ba zai karbi wani abu daga gare shi ba, kuma zai azabtar da shi a lahira, yana daga dalilan haka fadarsa madaukakin sarki.
﴿وَمَن یَبۡتَغِ غَیۡرَ ٱلۡإِسۡلَـٰمِ دِینࣰا فَلَن یُقۡبَلَ مِنۡهُ وَهُوَ فِی ٱلۡـَٔاخِرَةِ مِنَ ٱلۡخَـٰسِرِینَ﴾ Wanda ya nemi wanin musuulunci a matsayin addini to ba za a karba daga gare shi ba, shi kuma a lahira yana daga cikin asararruu.{85 :3}
Kuma Allah Madaukaki ya ce:(قُلْ يَا أَهْلَ الْكِتَابِ تَعَالَوْا إِلَىٰ كَلِمَةٍ سَوَاءٍ بَيْنَنَا وَبَيْنَكُمْ أَلَّا نَعْبُدَ إِلَّا اللَّهَ وَلَا نُشْرِكَ بِهِ شَيْئًا وَلَا يَتَّخِذَ بَعْضُنَا بَعْضًا أَرْبَابًا مِّن دُونِ اللَّهِ ۚ فَإِن تَوَلَّوْا فَقُولُوا اشْهَدُوا بِأَنَّا مُسْلِمُونَ) {Ka ce: "Yã ku Mutãnen Littãfi! Ku zo zuwa ga kalma mai daidaitãwa a Tsakaninmu da ku; kada mu bauta wa kõwa fã ce Allah. Kuma kada mu haɗa kõme da Shi, kuma kada sãshenmu ya riƙi sãshe Ubangiji, baicin Allah." To, idan sun jũya bãya sai ku ce: "ku yi shaida cẽwa, lalle ne mu masu sallamã wa ne}{64 :3}
MENENE YA WAJABA AKAINA DON IN ZAMA MUSLMI?
Imani da wadannan rukunai shida yana wajaba domin shiga musulunci:
Imani da Allah madaukaki, kuma shi ne mahalicci mai azurtawa mai tsarawa mamallaki, wani abu bai yi kama da shi ba, ba shi da mata ko Da, kuma shi kadai ya cancanci a bautawa.
Imani da mala'iku, cewa su bayin Allah madaukaki sarki ne, ya halicce su daga haske, ya kuma sanya daga cikin ayyukan su, suna saukowa da wahayi ga annabawansa.
Imani da dukkanin littattafai wadanda Allah ya saukar da su ga annabawansa (kamar Attaura da Injila) karshen littattafan shi ne Alkur'ani mai girma.
Imani da dukkanin manzanni, kamar annabi Nuhu da annabi Ibrahim da annabi Musa da annabi Isa, na karshensu shi ne annabi Muhamad, dukkaninsu daga 'yan adam suke, (Allah) ya karfafe su da wahayi ya kuma ba su ayoyi da mu'ujizozi, wadanda suke nuni akan gaskiyarsu.
Imani da ranar karshe, yayin da Allah zai tashi na farko da na karshe, Allah kuma ya yi hukunci tsakanin halittarsa, ya shigar da muminai Aljanna kafirai kuma ya shigar da su Wuta.
Imani da kaddara, cewa: Allah ya san komai, abinda ya kasance da kuma abinda zai kasance nan gaba, kuma hakika Allah ya rubuta haka, kuma ya ga damar hakan, ya halicci komai.
MUSULUNCI HANYA CE TA FARIN CIKI
Musulunci addinin dukkanin annabawa ne, ba addini ne da ya kebanci Larabawa kawai ba.
Musulunci shi ne hanyar samun farin ciki na hakika, a duniya da ni'ima madawwamiyya a lahira.
Musulunci shi ne addini guda daya, mai iko a bisa amsa bukatun rai da jiki, da warware (magance) matsalolin 'yan Adam.
Allah - Madaukakin sarki - Ya ce:
{قَالَ اهْبِطَا مِنْهَا جَمِيعًا بَعْضُكُمْ لِبَعْضٍ عَدُوٌّ فَإِمَّا يَأْتِيَنَّكُمْ مِنِّي هُدًى فَمَنِ اتَّبَعَ هُدَايَ فَلا يَضِلُّ وَلا يَشْقَى Ya ce: Ku sauka kũ biyu daga gare ta gabã ɗaya, sãshenku yanã maƙiyi ga sãshe. To, imma dai wata shiriya ta zo muku daga gare Ni, to, wanda ya bi shiryarwa ta, to, bã ya ɓacẽwa, kuma bã ya wahala.وَمَنْ أَعْرَضَ عَنْ ذِكْرِي فَإِنَّ لَهُ مَعِيشَةً ضَنْكًا وَنَحْشُرُهُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ أَعْمَى Kuma wanda ya bijire daga ambatõNa (Alƙur'ãni) to, lalle ne rãyuwa mai ƙunci ta tabbata a gare shi, kuma Munã tãyar da shi a Rãnar kiyãma yanã makãho.[124,123 :20}
ME ZAN AMFANA DAN GANE DA SHIGA MUSULUNCI?
Shiga musulunci yana da fa'idoji masu yawa, yana daga cikin su:
Rabauta da girma a duniya, wato mutum ya kasance bawa ga Allah. in ba haka ba ya kasance bawa ga san zuciya da shaidan da sha'awe-sha'awe.
Mafi girman rabo a lahira, ya tsira daga azabar wuta, ya kuma shiga aljanna, ya rabauta da yaddar Allah, da dawwama acikin aljanna.
Wadanda Allah zai shigar da su aljanna, za su rayu a cikin ni'ima ta har abada, ba mutuwa ko wani nau'i na rashin lafiya ko radadi ko bakin ciki ko tsufa, za su kuma sami dukkan abinda suke son shi.
Acikin Aljanna akwai abubuwan jin dadi, da idanu bai gansu ba, kunne bai ji su ba, ba kuma su darsu a zuciyar wani mutum ba.
Yana daga dalilan haka fadar sa madaukakin sarki:﴿مَنۡ عَمِلَ صَـٰلِحࣰا مِّن ذَكَرٍ أَوۡ أُنثَىٰ وَهُوَ مُؤۡمِنࣱ فَلَنُحۡیِیَنَّهُۥ حَیَوٰةࣰ طَیِّبَةࣰۖ وَلَنَجۡزِیَنَّهُمۡ أَجۡرَهُم بِأَحۡسَنِ مَا كَانُوا۟ یَعۡمَلُونَ﴾ Wanda ya aikata (aiki) na gari daga namiji ko mace alhalin yana mu'umini lalle za mu raya shi rayuwa mai dadi, kuma lalle za mu saka musu da ladan su da mafi kyan abinda suka kasance suna aikatawa.{97 : 16}
HASARAR ME ZAN YI IDAN NA KI MUSULUNCI?
Mutum zai yi hasarar mafi girman ilimi da sani, shi ne sanin Allah, kuma zai yi hasarar imani da Allah, wanda ya ke bawa mutum aminci da nutsuwa a duniya, da ni'ima madawwamiyya a lahira.
Mutum zai yi hasarar tsinkaye a bisa mafi girman littafi da Allah ya saukar da shi zuwa ga mutane, da kuma imani da wannan littafi mai girma.
Zai yi hasarar imani da annabawa masu girma, kamar yadda zai yi hasarar zama tare da su a aljanna ranar alkiyama, zai kasance abokin zaman shaidan da masu laifuffuka da dagutai (wadanda aka bautawa) a cikin wutar jahannama, tir da wannan gida kuma tir da wannan makotaka.
Allah - Madaukakin sarki - Ya ce:
قُلْ إِنَّ الْخَاسِرِينَ الَّذِينَ خَسِرُوا أَنْفُسَهُمْ وَأَهْلِيهِمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ أَلا ذَلِكَ هُوَ الْخُسْرَانُ الْمُبِينُ (15) Kace hakika hasararru su ne wadanda suka yi hasarar kawunansu da iyalan su ranar alkiyama, ku saurara, wannan ita ce hasara bayyananna.لَهُمْ مِنْ فَوْقِهِمْ ظُلَلٌ مِنَ النَّارِ وَمِنْ تَحْتِهِمْ ظُلَلٌ ذَلِكَ يُخَوِّفُ اللَّهُ بِهِ عِبَادَهُ يَا عِبَادِ فَاتَّقُونِ } . Sunã da waɗansu inuwõwi na wutã daga samansu, kuma daga ƙasansu akwai waɗansu inuwõwi. Wancan Shĩ ne Allah ke tsõratar da bãyinSa da shi. Yã bãyĩNa! To, ku bĩ Ni da taƙawa.{16, 15 :39)
Kada ka jirkinta (daukar) matsaya)
Duniya ba gidan dawwama ba ce...
Kowanne kyau zai bace daga gare ta, kuma kowacce sha'awa za ta bace...
Wuni zai zo wanda, za'a yi hisabi a cikin sa, akan dukkan abinda ka gabatar, shi ne ranar alkiyama, Allah madaukakin sarki ya ce:{وَوُضِعَ الْكِتَابُ فَتَرَى الْمُجْرِمِينَ مُشْفِقِينَ مِمَّا فِيهِ وَيَقُولُونَ يَا وَيْلَتَنَا مَالِ هَذَا الْكِتَابِ لاَ يُغَادِرُ صَغِيرَةً وَلاَ كَبِيرَةً إِلاَّ أَحْصَاهَا وَوَجَدُوا مَا عَمِلُوا حَاضِرًا وَلاَ يَظْلِمُ رَبُّكَ أَحَدًا} Kuma aka aje littãfin ayyuka, sai ka ga mãsu laifi sunã mãsu jin tsõro daga abin da ke cikinsa, kuma sunã cẽwa "Kaitonmu! Mẽne ne ga wannan littãfi, bã ya barin ƙarama, kuma bã ya barin babba, fãce yã ƙididdige ta?" Kuma suka sãmi abin da suka aikata halarce. Kuma Ubangijinka bã Ya zãluntar kõwa[49 : 18}
Hakika Allah mai girma da daukaka ya bada labari cewa, mutumin da bai musulunta ba, lalle makomar sa dawwama a cikin wutar jahannama har abada.
Hasarar ba mai sauki ba ce, a'a hasara ce mai girma.{وَمَن يَبْتَغِ غَيْرَ الْإِسْلَامِ دِينًا فَلَن يُقْبَلَ مِنْهُ وَهُوَ فِي الْآخِرَةِ مِنَ الْخَاسِرِينَ } {Kuma wanda ya nẽmi wanin Musulunci ya zama addini, to, bã zã a karɓa daga gare shi ba. Kuma shi a Lãhira yana daga cikin mãsu hasãra{85 : 3}.
Musulunci shi ne addini, wanda Allah ba ya karbar wani adddini daga addinai in ba shi ba.
Allah ya halicce mu, kuma zuwa gare shi mu ke komawa, wannan duniya jarrabawa ce a gare mu.
Ka sakankance: (tabbatar) cewa, wannan duniyar takaitacciya ce, misalin mafarki... babu wani da yasan yaushe ne zai mutu!
Menene zai kasance amsarka ga mahalaccinka ranar alkiyama: Me yasa baka bi gaskiya ba?me yasa baka bi cikamakin annabawa ba?
Me za ka amsawa Ubangijinka ranar alkiyama, ga shi ya gargadeka kada ka bi kafirci, ka bi hanyar musulinci, kuma ya baka labari cewa makomar kafirai halaka a cikin wuta har abada.
kuma Allah Madaukaki ya ce﴿وَالَّذِينَ كَفَرُوا وَكَذَّبُوا بِآيَاتِنَا أُولَئِكَ أَصْحَابُ النَّارِ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ﴾ Kuma waɗanda suka kãfirta, kuma suka ƙaryata game da ãyõyinMu, waɗannan sũ ne abõkan Wuta; sũ a cikinta madawwama ne.[2: 39]. {39 :2}
Babu wani uzuri ga wanda ya bar gaskiya, ya yi koyi da iyaye da kakanni.
Allah mai girma da daukaka ya bamu labari cewa: mutane da yawa suna kin shiga musulunci, don tsoran yanayi (al'ummar) da suke rayuwa a cikin ta.
Da yawa kuma suna kin musulunci, saboda ba sa son canza akidojin su, wadanda suka gaje su daga iyayen su, suka kuma saba da su, dayawa daga cikin su, taassubaci (riko) da barna wacce suka gaje ta yana hanasu shiga musulunci..
Wadannan gaba dayansu ba su da wani uziri akan haka, za su tsaya a gaban Allah ba tare da wata hujja ba.
Babu wani uzuri ga mai kore samuwar Allah wai ya ce: Zan tabbata akan (akidar) kore samuwar Allah, domin ni an haifeni acikin iyali masu kore samuwar Allah, a'a, ya jaba a kan shi ya yi amfani da hankalin da Allah ya ba shi, ya kuma lura da girman sammai da kasa, ya yi tunani da hankalinsa wanda mahaliccinsa ya ba shi, don ya gane cewa wannan kasantccen yana da mahalicci. Hakanan wanda yake bautawa duwatsu da gumaka ba shi da wani uziri na koyi da iyayensa, a'a yana wajaba akansa ya binciki gaskiya ya kuma tambayi kansa, yaya zan bautawa sandararrun abubuwa (marasa motsi) ba sa ji na, ba sa gani na, ba sa kuma amfanar da ni wani abu?!
Haka nan Banasare (Kirista) wanda ya yi imani da wasu abubuwa, da suka sababawa hankali da tunani, yana wajaba ya tambayi kansa: Ta yaya Ubangiji zai kashe dansa wanda bai aikata wani laifi ba, saboda zunuban wasu mutane daban! wannan yana daga zalunci!.Yaya zai yi wu ga 'yan adam su gicciye kuma su kashe dan ubangiji! Shin Ubangiji bai zamo ba mai iko ne akan ya gafarta zunuban 'yan adam ba tare da ya yi musu rangwame na su kahe dansa ba? shin ubangiji bai zamo mai iko ba a bisa ya kare dansa?
Abinda yake wajibi akan mai hankali ya bi gaskiya, kada ya yi koyi da iyaye da kakanni akan barna.
Allah - Madaukakin sarki - Ya ce:﴿وَإِذَا قِیلَ لَهُمۡ تَعَالَوۡا۟ إِلَىٰ مَاۤ أَنزَلَ ٱللَّهُ وَإِلَى ٱلرَّسُولِ قَالُوا۟ حَسۡبُنَا مَا وَجَدۡنَا عَلَیۡهِ ءَابَاۤءَنَاۤۚ أَوَلَوۡ كَانَ ءَابَاۤؤُهُمۡ لَا یَعۡلَمُونَ شَیۡـࣰٔا وَلَا یَهۡتَدُونَ﴾ Kuma Idan akace da su ku taho zuwa abinda Allah ya saukar, ku taho zuwa manzo (sai) su ce abinda muka sami iyayenmu akansa ya ishe mu, shin koda iyayen na su ba sa hankaltar wani abu, ba sa kuma shiryuwa.{104 : 5}.
WANDA YAKE SON YA MUSULUNTA KUMA YANA TSORAN KADA 'YAN'UWANSASU CUTARWAR DA SHI YA ZAI YI?
Wanda yake son ya musulunta, kuma yana tsroran jama'ar da take kewaye da shi, zai yi wu ya musulnta ya boye imaninsa, har zuwa lokacin da Allah zai yassare masa, wata hanya ta alkhairi da zai tsaya da kansa ya bayyanar da musulincinsa.
Yana daga wajibi a gare ka, ka karbi musulunci da gaggawa, sai dai ba ya wajaba a kanka ka bawa wadanda suke kewaye da kai labarin musuntarka, ko ka bayyanar da shi, idan hakan akwai cutarwa a gare ka.
Ka sani cewa, idan ka musulunta, zaka zamo dan uwa ga miliyoyin Musulmai, kuma zai yi wu ka sadu da masallaci ko cibiyar musulinci dake garinka, ka nemi shawararsu, da taimako, hakan zai faranta musu rai.
Allah - Madaukakin sarki - Ya ce:
{وَمَنْ يَتَّقِ اللَّهَ يَجْعَلْ لَهُ مَخْرَجًا وَيَرْزُقْهُ مِنْ حَيْثُ لَا يَحْتَسِب} Kuma wanda ya bi Allah da takawa zai sanya masa mafita kuma zai azurta shi daga inda ba ya zato,{3 ,2 :65}
Ya Kai Mai Karatu Mai Girma.
Shin yardar da Allah mahalincinka,-wanda ya yi ni'ima a gare ka, da dukkanin ni'imominsa, kuma ya kasance yake ba ka abinci, alhalin kana dan tayi, acikin mahaifiyarka, yake kuma azurta ka da iska wacce kake shaka yanzu- shi ne mafi mahimmanci daga yardar mutane a gare ka ?.
Shin rabon duniya dana lahira bai zamo ya cancanci bada dukkan abinda bai kai shi ba, na daga abubuwan jin dadi na duniya mai gaushewa? wallahi ya cancanta!
Kar ka bari abinda ya shude maka, ya hanaka gyara matafiyarka ta kuskure, da aikata abinda yake ingantacce.
Ka sance mu'umini na hakika a yau, kada kaba shaidan dama ya tsayar da kai bin gaskiya.
Allah - Madaukakin sarki - Ya ce:
{يَا أَيُّهَا النَّاسُ قَدْ جَاءَكُمْ بُرْهَانٌ مِنْ رَبِّكُمْ وَأَنزلْنَا إِلَيْكُمْ نُورًا مُبِينًا (174) Yã kũ mutãne! Haƙĩƙa wani dalĩli daga Ubangijinku yã zo muku kuma Mun saukar da wani haske, bayyananne zuwa gare ku.فَأَمَّا الَّذِينَ آمَنُوا بِاللَّهِ وَاعْتَصَمُوا بِهِ فَسَيُدْخِلُهُمْ فِي رَحْمَةٍ مِنْهُ وَفَضْلٍ وَيَهْدِيهِمْ إِلَيْهِ صِرَاطًا مُسْتَقِيمًا (175) } To, amma waɗanda suka yi ĩmãni da Allah kuma suka yi riko da Shi, to, zai shigar da su cikin wata rahama daga gare Shi da wata falala, kuma Ya shiryar da su zuwa gare Shi ga tafarki madaidaici.{175, 174 :4}
Shin ka shirya don daukar mafi girman mataya a rayuwarka?
Idan dukkan wannan abinda ya gabata ya kasance dalilai ne na hankali a gare ka, kuma ka yi furici da hakika, a zuciyarka, to, ya wajaba a gare ka, ka yi bi mataki na farko, ka musulunta, shin kana son in taimaka maka, abisa daukar mafificin matsaya a rayuwarka da kuma shiryar da kai zuwa yadda za ka musulunta?.
Kada ka sanya zunubanka su hana ka shiga musulunci, hakika Allah ya ba mu labari a cikin Alkur'ani cewa, shi yana gafarta zunuban mutum baki daya, idan ya musulunta ya tuba ga mahaliccinsa, harma bayan ka karbi musulunci. A dabi'ance kai zaka aikata wasu zunubai, mu yan adam ne ba mala'iku ba ne ababan tsarewa, sai dai abinda ake nema daga gare mu, mu nemi gafara daga Allah mu kuma koma zuwa gare shi, idan Allah ya ga ka yi gaggawar karbar gaskiya ka shiga musulunci, ka yi furuci da kalmar shahada biyu, to, hakika shi zai taimake ka abisa barin zunubai, wanda yake fuskantar Allah yake kuma bin gaskiya, Allah zai datar da shi ga karin alkhairi, kada kai kokwantan shiga musulunci a yanzun nan.
Yana daga dalilan haka fadarsa madaukakin sarki:﴿قُل لِّلَّذِینَ كَفَرُوۤا۟ إِن یَنتَهُوا۟ یُغۡفَرۡ لَهُم مَّا قَدۡ سَلَفَ﴾ Kace da wadanda suka kafirce in suka hanu (suka bar abinda suke yi na kafirci) za'a gafarta musu abinda ya shude.{38 : 8}.
ME ZAN YI DON IN ZAMA MUSULMI?
Shiga musulunci lamarinsa mai sauki ne, ba ya bukatuwa zuwa al'adu (na biki) ko wasu abubuwa na musamman, ko sai a gaban wani, abida kawai yake kan mutum kawai, ya yi furici da shahada biyu, yana mai sanin ma'anarsu, yana kuma mai imani da su. Hakan kuwa shi ne ya ce: (Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, ina kuma shaidawa hakika annabi Muhammad manzon Allah ne) in ya saukaka a gare ka, ka fada da harshen larabci yana da kyau, idan kuma hakan zai wahala a gare ka, to, ya isa ka yi furici da su, da harshenka, da hakan za ka kasance musulmi, sannan yana wajaba akanka, ka koyi addininka, wanda shi ne asalin farin cikinka a duniya da kuma tsirarka a lahira.
Don neman karin bayani dangane da musulunci, ina yi maka wasiyya da shiga shafin:
Mai hada (likau) fassarar ma'anonin Alkur'ani mai girma da harshen......:
Domin kuma kasan yadda za ka gudanar da musulunci, muna yi maka wasiyyar shiga shafin:
WANENE YA HALICCE NI? KUMA SABODA ME?Ko wanne abu yana nuni akan akwai mahalicci
Allah Mai tsarki kuma Madaukaki
Suffofin Ubangiji tsarkakakke madaukaki
Ubangiji abin bautawa, babu makawa lalle ya siffantu da siffofin cika
Shin zai yi wu a hankalce mahalicci ya bar mu, ba tare da wahayi ba?
ME YASA MANZANNI SUKE DA YAWA?
Mutum ba zai kasance mumini ba, har sai ya yi imani da dukkanin manzanni
ME MUSULMAI SUKE KUDIRCEWA DANGANE DA ANNABI ISA AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARE SHI ?
MENENE YA WAJABA AKAINA DON IN ZAMA MUSLMI?
MUSULUNCI HANYA CE TA FARIN CIKI
ME ZAN AMFANA DAN GANE DA SHIGA MUSULUNCI?
HASARAR ME ZAN YI IDAN NA KI MUSULUNCI?
Kada ka jirkinta (daukar) matsaya)
Babu wani uzuri ga wanda ya bar gaskiya, ya yi koyi da iyaye da kakanni.
WANDA YAKE SON YA MUSULUNTA KUMA YANA TSORAN KADA 'YAN'UWANSASU CUTARWAR DA SHI YA ZAI YI?
Shin ka shirya don daukar mafi girman mataya a rayuwarka?
ME ZAN YI DON IN ZAMA MUSULMI?